ABNA24 : Rahotannin dai sun ce a wani lokaci a yau ɗin nan Alhamis ne ake sa ran tsohon shugaba Gbagbon zai baro birnin Brussels zuwa birnin Abidjan ɗin bayan da a wani lokaci a baya Kotun ƙasa da ƙasa mai shari’ar manyan laifuffuka ICC da ke birnin Hague ta tabbatar da wanke shi daga zargin da ake masa shi da tsohon ministansa na matasa Charles Ble Goude na laifuffukan yaƙi da cin zarafin bil’adama.
Ana zargin mutane biyun ne dai da hannu cikin rikicin da ya faru a ƙasar Ivory Coast bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a shekara ta 2011 da yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
A daidai lokacin da wasu suke ganin komawarsa gida ɗin bayan ya shafe kusan shekaru 10 a tsare a matsayin wani lamari da zai kara munana irin zaman doya da manja da ake yi a ƙasar, sai dai kuma magoya bayansa suna ganin dawowarsa ɗin zai taimaka wajen magance waɗannan matsalolin.
Shugaban ƙasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya ba da umurnin a shirya masa tarbar irin ta shugaban ƙasa kamar yadda kuma ya ba da umurnin a ba shi dukkanin girmama da kuma haƙƙoƙin da ake ba wa tsoffin shugabannin ƙasar.
342/